9 Agusta 2021 - 14:37
Iran Ta Yi Watsi Da Tuhumar Da Kasashe Masu Karfin Tattalin Arziki 7 Suke Mata

Mir Husain Qadhizade Hashimi wani dan majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa, maimakon nanata tuhumar kasar Iran ta kai hari kan wani jirgin ruwan HKI a tekun Oman, kamata yayi kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya su bayyana dalilinsu na wannan tuhumar.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto Qadhizade Hashimi yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa sanarwar da wadannan kasashe 7 suka fitar a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ba ta da wani muhimmanci matukar ba wani dalili da hujja a fili na abin da suke tuhumar kasar ta Iran.

Labarin ya kara da cewa a makon da ya gabata ne wasu kafafe yada labarai suka ba da labarin cewa wani jirgi sama wanda ake sarrafa shi daga nesa ya kai hari kan wani jirgin ruwa mallkin wani dan HKI, ya kuma yi sanadiyyar mutane kasashen Turai guda biyu.

Sannan a ranar Alhamis da ta gabata wadannan kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya suka fidda bayani wanda yake tuhumar gwamnatin kasar Iran da hannun a cikin harin, amma ba tare da bayyana wani dalili ba.

342/